Ephesians 4

1Saboda haka a matsayi na na dan sarka saboda Ubangiji; ina rokon ku ku yi zaman rayuwa da ta cancanci kiran da Allah ya kiraye ku. 2Ku zamna da matukar tawali’u da sahihanci da hakuri. Ku karbi juna cikin kauna. 3Ku yi kokarin zaman dayantaka cikin Ruhu kuna hade cikin salama.

4Akwai jiki daya da kuma Ruhu daya, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan daya. 5Ubangiji daya, bangaskiya daya, da kuma baftisma daya. 6Allah daya ne da Uban duka. Shine bisa duka, ta wurin duka, da kuma cikin duka.

7Ko wannenmu an ba shi baiwa bisa ga awon baiwar Almasihu. 8Kamar yadda nassi ya ce, “Da ya haye zuwa cikin sama, ya bi da bayi cikin bauta. Ya kuma yi wa mutane baye baye.

9Menene ma’anar,, “Ya hau?” Ana cewa kenan ya sauka har cikin zurfin kasa. 10Shi da ya sauka shine kuma wanda ya hau birbishin sammai. Ya yi wannan domin ya cika dukan abubuwa.

11Almasihu ya ba da baye baye kamar haka: manzanni, annabawa, masu shelar bishara, makiyaya, da masu koyarwa. 12Ya yi haka domin ya shiryar da masu bi saboda hidima, domin gina jikin Almasihu. 13Ya yi haka har sai mun kai dayantakar bangaskiya da sanin Dan Allah. Ya yi haka har sai mun kai ga manyanta, kamar wadanda suka kai cikakken matsayin nan na falalar Almasihu.

14Wannan ya zamanto haka domin kada mu kara zama kamar yara. Kada a yi ta juya mu. Wannan haka yake domin kada mu biye wa iskar kowacce koyarwa ta makirci da wayon mutane masu hikimar yin karya. 15Maimakon haka za mu fadi gaskiya cikin kauna domin mu yi girma cikin dukan tafarkun da ke na sa, shi da yake shugaba, Almasihu. 16Almsihu ya hada dukan jikin masu ba da gaskiya. Jikin yana hade ta wurin kowanne gaba, domin jikin ya yi girma ya gina kansa cikin kauna.

17Saboda haka ina yi maku gargadi cikin Ubangiji cewa, kada ku sake yin rayuwa irin ta al’ummai da suke yi cikin azancin wofi marar amfani. 18Sun duhunta cikin tunaninsu. Bare suke da rai irin na Allah, ta wurin jahilcin da ke cikinsu da ta wurin taurare zukatansu. 19Basa jin kunya. Sun mika kansu ga mutumtaka ta yin kazamtattun ayyuka da kowacce zari.

20Amma ba haka kuka koyi al’amuran Almasihu ba. 21Ina zaton kun rigaya kun ji a kansa. Ina zaton an koyar da ku cikinsa, kamar yadda gaskiyar Yesu ta ke. 22Dole ku yarda halin ku na da, wato tsohon mutum. Tsohon mutumin ne ya ke lalacewa ta wurin mugun buri.

23Ku yarda tsohon mutum domin a sabonta ku cikin ruhun lamirinku. 24Ku yi haka domin ku yafa sabon mutum, mai kamanin Allah. An hallitta shi cikin adalci da tsarki da gaskiya.

25Saboda haka ku watsar da karya. “Fadi gaskiya ga makwabcin ka”, domin mu gabobin juna ne. 26“Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi.” Kada ku bari rana ta fadi kuna kan fushi. 27Kada ku ba shaidan wata kofa.

28Duk mai yin sata, kada ya kara yin sata kuma. Maimakon haka, ya yi aiki. Ya yi aiki da hannuwan sa domin ya sami abin da zai taimaka wa gajiyayyu. 29Kada rubabbun maganganu su fito daga cikin bakinku. Maimakon haka, sai ingantattu da za su ba da alheri ga masu ji. 30Kada ku bata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai domin ta wurin sa ne aka hatimce ku domin ranar fansa.

31Sai ku watsar da dukan dacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da reni tare da dukan mugunta. Ku yi wa juna kirki, ku zama da taushin zuciya. Ku yafe wa juna, kamar yadda Allah cikin Almasihu ya gafarta maku.

32

Copyright information for HauULB